Home Labarai Shugaban Kasa Tinubu da Tallafin Man Fetur

Shugaban Kasa Tinubu da Tallafin Man Fetur

by masta

ALFANUN CIRE TALLAFIN MAN FETUR DA SHUGABA TINUBU YA YI.

Daga: Hassan Muhammed Marke

Haraji da tallafi suna daga cikin dabaru mafiya shuhura da gwamnati ke amfani dasu wurin nuna tasirinta a cikin al’amurran gudanarwar tsimi, tattali da tanadi. Shi dama haraji tun somu duniya akwai shi. Domin ta hanyar harajine gwamnati ke samun asalin kuÉ—aÉ—en shiga. Amma kuma bayan samun kuÉ—in shiga, gwamnati tana amfani da haraji don sagewa wata harka gwiwa a fakaice. Misali, idan gwamnati tana so a rage yawan shan taba sigari, sai ta zanbaÉ—awa kamfaninnikan sigari haraji. Ta hakan sai su rage koma su daina sarrafata gaba É—aya. Ta hakan an samu kuÉ—i kuma an dakatar da harkar. A akasin haka kuma gwamnati tana amfani da tallafi domin Æ™arawa wata harka karsashi. Misali, idan gwamnati tana so a ringa shan lemon Pop Cola, zata iya ware wasu kuÉ—i ta bawa masu kamfanin wanda zai basu damar zabtare farashin lemon zuwa mataki mai rahusar da zasuyi ta saye. Ta wata hanyar kuma zata iya yafewa kamfanin lemon harajin shekaru uku, su kuma sai su rage farashin zuwa yadda mutane zasu iya saya. Wannan duka misaline!

Akan batun man fetur gwamnatin Nijeriya ta gano cewa mutane bazasu ji daɗin sayensa ba har sai ta tasiranci farashinsa. Ta yaya take iya yin hakan? Ta hanyar ware wasu maƙudan kuɗaɗe daga cikin lalitar kasafin ƙasa ta bawa masu kasuwanci da tace man feturin don su matso da farashin zuwa matakin da talaka zai ji daɗin saye. Gwamnatin shugaba Tinubu tunda aka rantsar das ya ke ƙoƙarin dai daita farashin da talaka zaiji daɗin abinsahi.

Kwatsam sai Allah ya kawo mu wani lokaci wanda abinda yake kawowa Æ™asarmu kuÉ—in shiga, wato É—anyen mai, ya karye warwas a kasuwar duniya. Wanda kai tsaye hakan yana nufin lalitarmu bazata riÆ™a samun yawan kuÉ—aÉ—en shiga kamar na baya ba. Kuma gashi an riga an saba da rayuwar jin daÉ—i, irinta masu hali da sukuni, ana bawa yan Æ™asa tallafin mai, gashi kasafin Æ™asa duk shekara yana nuna kuÉ—aÉ—e masu nauyi da aka warewa salon mulki da gudanarwa, wanda maimakon su ragu sai Æ™aruwa suke yi, gashi kuma yanzu babu kuÉ—in shigar da za’a yi irin wannan rayuwa.

Kamar mutum ne wanda yake cin ₦aira dubu É—ari a wata, sai kwatsam albashinsa ya dawo ₦aira dubu arba’in sakamakon canzawar yanayin aiki. A baya sanda yake cin dubu É—ari ana cin naman kaza da lemon gwanda, a kunna janarero a kalli wasan kwaikwayo sannan a bawa uwargida tallafin dubu biyar ta sayi datar hawa yanar gizo-gizo da Æ™arin wata dubu goman a taimakawa iyaye da Æ´an uwa da suke Æ™auye.

Daga baya shugaba Tinubu yayi nazari akan tattalin arziÆ™inmu, lokacin da kuÉ—in shigarmu ya shiga halin ha’ula’i, sai shugaba Tinubu yayi ganawar sirri da masana tattalin arziÆ™in Æ™asar mu, A kalaman shugaba Tinubu ya ce menene abinda ya dace a cire daga kasafin Æ™asa wanda muhimmancinsa bai kai na sauran ba. Idan yaso sai a cire don talakawa su samu sauÆ™in halinda suke ciki.

Misalin kamar wancan mutumine da ya dawo cin dubu arba’in. Idan yana da hankali zai duba ya ga a cikin uzuran gidansa me ya kamata a cigaba wanne ya kamata a dakatar. Sai akayi rashin sa’a maigida wawane, maimakon yayi hakan, sai yaje ya ringa ciyo bashin banki yana cike gurbin abinda ya rasa a albashinsa, aka cigaba da cin naman kaza, ana kunna janareto, ana sayawa uwargida data ana turawa yan uwa kuÉ—i Æ™auye, har saida takardar banki ta nuna ya tsunduma cikin bashin da babu ranar biya. Yanzu kuma ya farka daga mafarkin shirme, yana so ya dakatar da waccan ta’asa.

Babban abin lura anan shine; gwamnatin Shugaba Tinubu ta sa hankalinta akan wannan halin da ƴan ƙasa suke ciki na wahalar rayuwa Inda yace ai tunda kiɗa ya canza dole rawa ta canza, ayi haƙuri a ara mini lokaci, jawabin bai ƙare anan ba!

Shin yayi daidai idan aka cire tallafin man fetur?

Wannan itace tambayar da kowa yake son yaji amsarta. Kuma yadda abun yake shine; babu wani mai hankali da zai ringa cin bashi yana sayen naman kaza yana ci. Koh kuma ya ringa cin bashi yana taimakawa yan uwansa bayan cewa bashi da sukunin yin hakan. Tallafin man fetur, idan zamu faÉ—awa kanmu gaskiya, kamar haka yake. Kai tsaye baya É—aya daga cikin wajibai irinsu lafiya, ilimi, tsaro, masarufi, ababan more rayuwa dss, duk da cewa a kaikaice yana tasirantar kowannensu. Dalili kuwa shine, shi bashi ana cinsa ne kawai idan za’ayi amfani da kuÉ—in da aka ciyo akan turbar samun wasu kuÉ—in da zasu taimaka a biya bashin, kamar ilimi, masana’antu, lafiya, tsaro dss, ba wai akan abinda kai tsaye zai tafi masai ba. Ciyo bashi a aiwatar da salon mulki mai tsada dai-dai yake da ciyo bashi aci naman kazar da zai tafi masai. Hakama ciyo bashi a biya tallafin mai daidai yake da ciyo bashi a taimakawa Æ´an uwa. Dukkaninsu ba wajibi bane. Wannan shine jawabin masana tattali arziÆ™in Æ™asa suke faÉ—i a taron da shugaba Tinubu yayi.

A zahirin gaskiya, idan biyan tallafin man fetur ba wajibi bane kyautatawa ce da za’a iya cirewa a lokacin matsi, toh salon mulki mai tsada ma makaruhine wanda yinsa babu laifi amma barinsa ma yafi aiwatar dashi natija, musamman a lokacin matsi. Bazai taÉ“a yin ma’ana ba idan aka cire tallafin man fetur domin ragewa Æ™asa nauyin bashi.

Me yasa nace haka?

Lokacin da muke ciki lokacine da ake fuskantar barazanar hauhawar farashin kayan masarufi mafi tsauri a tarihi sakamakon lokacin ne na hauhawar kayan abinci a duniya baki É—aya. Akwai Æ™arancin aikin yi. Darajar kuÉ—inmu tana faÉ—uwa. Amma gashi yanzu Shugaba Tinubu ya É—auko wata hanya ta magance su. Shugaba Tinubu ya Æ™ara cewa cire tallafin man fetur a wannan yanayi, zai Æ™ara hautsina farashin kayayyaki, duba da yadda sufuri da masana’antu suka dogara kacokam akan amfani da man fetur, illa Æ™alilan daga ciki, Amma Æ´an Æ™asa zasuji daÉ—i nan gaba kaÉ—an. Hauhawar farashin man fetur yana nufin hauhawar farashin aiwatar da sufuri da masana’antu, wanda suma dole su fanshe a wurin masu sayen kayayyaki da ayyukansu. Hakan na nuna cewa kafin Æ™iftawa da bismillah kayan masarufi zasu Æ™ara tashin gwauron zabo, Kuma hakan akwai alkhairi nan gaba kaÉ—an.

Mahangar Shugaba Tinubu akan kasuwancin man fetur itace a yanzu. Yana ganin cewa idan ya cire tallafi Æ´an kasuwa zasu samu lasisin hankaÉ—o shi cikin kasuwanni ba tare da birki ba. Wanda kuma idan hakan ta faru za’a samu gasa a tsakaninsu wadda zata sanya wanda yake son ya sayar akan lokaci dole ya zabtare farashi zuwa matakin da zai ja hankalin jama’a. Idan kuma hakan ta faru masu gasa dashi zasu so su wuce, don haka sai suma su zabtare nasu farashin. Ta hakan, gwamnati tana ganin, gasa zata sanya man fetur ya dawo farashi mai sauÆ™i ga talakawa.

Ƙasar Amurkan da muke kwaikwayo a lokacin da muke ciki a yanzu. A lokacin shugabanni Kennedy, Nixon da Reagan duk an samu hauhawar farashi da rashin aikin yi. A lokacin Nixon masana ne, Wanda suke faÉ—awa wani shugaba da Æ™asar sa ta shiga irin wannan yanayin da Æ™asar mu Nigeria ta ke ciki, suke cewa, Idan yace zai magance rashin aikin yi hauhawar farashi zata ninku, idan kuma yace zai magance hauhawar farashi rashin aikin yi zai ninku, sai abun ya bashi ciwon kai; gaba tsini baya siyaki. Can sai aka gano cewa idan aka tsai da farashi ba tare da an Æ™arawa ma’aikata albashi ba, farashi zai daidaita, kuma za’a samu aikin yi. Kuma haka ya aiwatar aka ga alfanu a kas!

Rigimar da Æ™asar mu zata shiga a yanzu ita ce: idan ba’a cire tallafin man fetur ba (koh kuka wani abun a makamancinsa) Nijeriya zata Æ™ara yawan bashin da zai iya mai damu kamar Æ™asar Girka – wanda idan hakan ta faru zamu shiga uku mu lalace – idan kuma aka cire za’a samu Æ™arin matsi da hauhawar farashi. Yanzu ya za’ayi kenan?

Sai Shugaba Tinubu yayi tunanin cewar shi talakawa ne suka zaÉ“e shi kuma sauÆ™i ya ke nema musu. Sai ya ce a dubi abinda ya ke cinye kudin Æ™asa a zabtare shi, sai a saka tallafin fetur É—in a madadinta, da sharadin cewa bayan farashi ya daidaita (tun da suna mafarkin yiwuwar hakan, za’a cire tallafin gaba É—aya. Ta hakan, baza’a Æ™arawa mutane matsi ba, kuma Nijeriya bazata Æ™ara nutsewa a cikin bashi ba.

A gaba ɗaya wannan tattaunawar shine yanzu lalitar Nijeriya bata da ƙarfin da zata biya tallafin abinda bazai dawo da riba ba kamar tallafin man fetur, amma kuma akwai abubuwan banza dana wofin da basu kai tallafin man fetur amfani ba da ake bawa tallafi mai yawa inji shugaba Tinubu.

A Æ™arshe shugaba Tinubu ya Æ™ara cewa Æ´an Nigeria su Æ™ara haÆ™uri akan cire tallafin man fetur da akayi. Wanda daga Æ™arshe za’a ga alfanun cire tallafin man fetur É—in.

#RenewedHope

Related Posts

Leave a Comment