Home Labarai Shugaban Kasa Malam Asiwaju Bola Ahmed Tinubù Zai Gyara Najeriya Da Zata Yi Gogayya Da Manyan Kasashen Duniya Irin Su Amurka Da Rasha

Shugaban Kasa Malam Asiwaju Bola Ahmed Tinubù Zai Gyara Najeriya Da Zata Yi Gogayya Da Manyan Kasashen Duniya Irin Su Amurka Da Rasha

by masta


DAGÀ Bashir Abdullahi El-bash

Lokacin da ya zama gwamnan Jihar Legas a 1999 Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya samu nasarar bunƙasa harajin Jihar daga Naira Miliyan 600 duk wata, zuwa Naira Biliyan 8.2 a 2007. A daidai wannan lokacin da Nageriya ta ke cikin matsayin tattalin arziƙi, ta na buƙatar Asiwaju wanda ya ke da ƙwarewa da dabarun bunƙasa tattalin arziƙi domin samun mafita ga yan kasa.

Shùgaba Tinubù ya samar da tsarin kiwon lafiya kyauta ga yara ƴan shekaru 18 da kuma tsofafafi ƴan shekaru 65. Ƴan Nageriya na buƙatar irin wannan tsari a daidai wannan lokaci, da Bola ya zama shugaban ƙasa.

Baya da wannan, Asiwaju ya kafa kwamiti na tawagar aiki wacce ta duba matsalolin lafiya a Jihar. Inda aka samar da tsarin ragewa mutane kuɗin magani su ke sayensa da sauki. Ya kuma samar da tsarin kula da lafiyar Ido na musamman inda aka gyarawa miliyoyin al’ummar Jihar Legas idanuwa su ke gani sosai tare da raba musu gilashin ƙarfin gani. Sannan ya kuma samar da tsarin magance matsalar cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS da na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da sauran muhimman tsare-tsare a fannin lafiya.

Shi ne ya samar da tsarin gine-gine na gidaje 500 duk shekara tare da kyautata harkokin gine-gine da gidaje gami da raya birnin Legas. Hakan kuma ya taimaka wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa birnin inda harkokin kasuwanci su ka ƙara samun cigaba. Wannan tunani ya na da kyau ƴan Nageriya su ba wa Shùgaban kasa hadin kai ya ƙara ɗaɓɓaƙa irinsa a ƙasa gaba ɗaya domin amfanin kowa da kowa.

Sannan kuma ya samar da shirin gina gidajen malamai da na ma’aikata da na alƙalai. Masu ɗauke da abubuwan ƙawa na alfarma. Wanda hakan ya buɗe babin samar da guraben ayyukan yi kimanin guda dubu 100.

A fannin sufuri ma ya zamanantar da harkar tafiye-tafiye da zirga-zirgar ababen hawa, gami da samar da hukuma ta musamman mai kula da ɗa’a da tarbiyar al’umma masu tuƙa ababen hawa. Irin tsarin da Nageriya na buƙatar wannan tunani nasa a yau domin samar da cigaba a fannin.

Haka kuma ya samar da sabbin makarantu musamman ma Firamare da sakandire tare da sabunta waɗanda ake da su daidai da tsarin zamani gami da inganta tsarin ba da horo na musamman ga malamai da kyautata albashinsu tare da biyan kuɗin jarabawar gama sakandire WAEC da NECO kyauta.

A shekarar 1999 zuwa 2003, ya yi rukunin gine-gine guda 22 a makarantun sakandire 15 akan kuɗi Naira 130,000,00. Kana kuma a dai wannan lokaci ya sabunta rukunin ajujuwa guda 39 akan kuɗi Naira 108,689,939. A 2003 ya samar da ƙarin sabbin makarantun sakandire guda 10. Ya gina ajujuwa guda 501 a makarantu 24 da makarantun sakandire 26. Ya sabunta wasu ajujuwa 602 a makarantun firamare 4 da makarantun sakamdire 50 tare da zuba kayan aiki da na jin daɗin ɗalibai.

Sannan ya samar da tsarin inganta tsaro da wadatacciyar wutar lantarki waɗanda su ka ƙara taimakawa wajen inganta zaman lafiya da tattalin arziƙin Jihar Legas. Duk waɗannan tsare-tsare ne waɗanda Nageriya ta ke buƙatar irinsu a yau, da muke da tabbacin cewa sabon shugaban kasa Asiwaju zai yi ƙoƙarin samar da irin wannan tsare-tsare. Waɗanda har lambobin yabo ya samu a kansu.

Related Posts

Leave a Comment