Shugaba Bola Tinubu, ya mayar da martani kan rikicin siyasa da ke kokarin kunno kai a Jamhuriyar Nijar, inda ya bayyana goyon bayansa ga zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya a kasar.
Yayin da rikici a Jamhuriyar Nijar ke kara kunno kai, Tinubu a madadin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ya jaddada aniyarsa na tabbatar da dimokuradiyya da tsarin mulki a kasar da ke fama da rikici.
Tinubu ya jaddada cewa yankin zai tsaya tsayin daka wajen goyon bayan zababbiyar gwamnati a Nijar.
Ya jaddada muhimmancin kiyaye dimokuradiyya ga alāummar Nijar da zaman lafiya da ci gaban yankin yammacin Afirka baki daya.
Ya ce, āBayanan da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa wasu abubuwa marasa dadi na faruwa a kan manyan shugabannin siyasar kasar. āYa kamata duk wadanda suke da hannu a lamarin sun san cewa shugabannin yankin ECOWAS da duk masu kaunar dimokuradiyya a duniya ba su goyi bayan wannan lamari ba.
āShugabannin ECOWAS ba za su amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga halaltacciyar gwamnatin Nijar ko wani yanki na yammacin Afirka ba.
āIna so sanar da cewa muna sa ido sosai kan alāamura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu, ta bunkasa, da tushe mai kyau a yankinmu.
āIna tuntubar sauran shugabannin yankinmu, kuma za mu kare dimokuradiyyar da muke buri bisa kaāidar tsarin mulki wanda kowa ya yarda da shi.
āA matsayina na shugaban kungiyar ECOWAS, ina jadadda aniyar goyon bayan Nijeriya ga zababbiyar gwamnati a Nijar, sannan ina tabbatar da cewar shugabannin ECOWAS ba za su bar Nijar cikin jimami ba, sai mun tsaya tsayin daka don kiyaye tsarin mulkin kasa


