Haƙiƙa, labarin hamshaƙiyar Uwa shahararre ne wajen jan hankalin makaranta, da ilimantarwa tare da koyar da wasu manya-manya sinadaran zaman aure a wannan zamani namu.
Wajibi ne mu jinjinawa marubuciya Halima K Mashi bisa wannan namijin kokari da tayi wajen samar da shahararren labari mai ɗauke da shahararrun darussa a mafi kyautatuwar salo da siga ingantacciya.
Na ƙayatu da yadda naga makarantan labarin sun cika da kukan idanuwa bisa shauƙin da labarin ya sanya su. Daman wannan shi ake kira da labari mai taɓa zuciya (interesting story), wanda mafi yawan marubuta suke da ƙalubale wajen samar dashi.
A ƙarshe ina kira da makaranta suyi amfani da damar karanta wannan labari tare da ɗabbaƙa darussan dake cikinsa. Dafatan Allah ya bamu dacewa baki ɗaya amin
Hajiya Halima K Mashi Allah ya Kara basira Amin


