Home Labarai Yadda rashin tsaro ke tasar da Gari

Yadda rashin tsaro ke tasar da Gari

by masta


Wasu Garuruwa Kan Zama Kufai A Sakamakon Ayyukan ‘Yan Ta’adda.
Gari Gobirawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da ‘yan bindiga suka mayar kufai, bayan yawan kai hare-haren ta’addanci da yayi tsamari.
Gobirawa na cikin yankin garin Kamfanin Doka da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kuma gari ne da yake da albarkar ƙasar noma. Garin Gobirawa na kudancin garin Doka, kilo mita shida.
Wannan ƙauye ya kasance ƙaramin gari ne wanda mazauna cikinsa sukai shuhura wajen noma da kiwo, haka zalika suna noman rani sakamakon rafin dake makwaftakata dasu. Duk da cewa basu da kyakkyawar hanya da wutar lantarki, su kan yi amfani da Babura masu ƙafa biyu wajen zirga-zirgarsu ta yau da kullum.
A yayin zantawarmu da wasu daga cikin mazauna wannan ƙauye na Gobirawa, sun bayyana cewa, “Yawan kai musu hare-hare da ‘yan bindiga ke yi, tare da ɗaukar mutane su nemi kuɗin fansa maƙudai ne yasa su barin ƙauyen, inda suka dawo cikin garin Doka, yayin da a nan ma yawan shigowar da ‘yan bindigar ke yi yasa wasu suka ƙara matsawa gaba suka koma Kaduna, wasu kuma suka koma ƙaramar hukumar Kontagora da ke jihar Niger.
Sun ƙara da cewa, “Kafin maharan sun tarwatsa musu gari, sun fara ne da zuwa suna kore musu dabbobi, kuma su kan zo ne da rana ko dare, ko duk lokacin da suka ga dama. Baya ga kore dabbobinsu, sai suka fara ɗaukar mutane, ko idan sun ga macen da tayi musu su haɗa da ita. Bayan sun tafi da waɗanda suka ɗiba sai kuma su nemi kuɗin fansa, idan ba a biya ba har kashe wanda suka ɗauka suke yi, sannan idan suka sake dawowa su kan yi ta’addanci fiye da na baya.”
Mazauna wannan ƙauye dai sun ce dole ce tasa suka haƙura da garin suka bar shi, wanda a yanzu ya riga ya zama kufai.
A yayin haɗa wannan rahoto, na ziyarci wannan ƙauye na Gobirawa, kuma a lokacin da naje na tarar da gidajen wannan ƙauye duk sun rushe, babu sauran koda rufaffen ɗaki guda ɗaya. Haka zalika wasu ɗakunan da suka rushe duk sun riga sun baje sai ɗan ɓirɓishinsu kaɗan da ba a rasa ba.
A da mazauna wannan ƙauye ba su ɗebe tsammanin komawa garin nasu ba, amma yanzu sun ce “Noman da suke zuwa suna yi ma don ya zame musu dole ne, saboda gonakinsu da suke wajen, amma duk da haka har yanzu suna fuskantar barazanar ‘yan bindiga musamman idan amfanin gona ya girma yayi duhu…” Daga Kaduna: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment