Home Labarai Direbobi na na kauracewa hanyar Funtua zuwa Birnin Gwari

Direbobi na na kauracewa hanyar Funtua zuwa Birnin Gwari

by masta

Yadda Direbobi Suka Ƙauracewa Hanyar Funtua Zuwa Birnin Gwari.

Hanyar Birnin Gwari da ta tashi daga Funtua, tsohuwar hanya ce da ta shafe shekaru da dama al’umma na amfani da ita, kama da fatake ‘yan kasuwa da jama’a masu balaguro zuwa wasu garuruwa da suka haÉ—ar da: Tegina, Kontagora, Manigi, Bidda, Niger, Makwa, Ibadan har zuwa Lagos.

To sai dai lamarin rashin tsaro yasa hanyar shiga cikin mawuyacin halin da aka shafe shekaru sama da bakwai ana tsoro tare da fargabar bin ta. Hakan kuma ya faru ne sakamakon ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane.

Al’amarin bai tsaya a kan Direbobi da matafiya kaÉ—ai ba, hatta da wasu Æ™auyukan dake wannan hanya ta shafe su, domin sai da ta kai mutanen dake zaune a garuruwan dake kan wannan babbar hanya Æ™auracewa gidajensu saboda yadda ‘yan bindigar suka addabe su.

Hakan yasa hanyar wadda ta taso daga Funtua zuwa Birnin Gwari ta zamo fes, babu mai amfani da ita sai su ‘yan bindigar, hakan ya jawo taÉ“arÉ“arewar harkokin kasuwanci a wannan yanki. Kamar yadda wasu mazauna yankin Funtua da Birnin Gwari suka bayyana.

Wani mazaunin yankin da ya buÆ™aci a sakaye sunansa, ya shaida wa wakilin IDON GARI cewa, “Bayan Æ™aurewa hanyar da direbobi suka yi na tsawon lokaci, su ‘yan bindigar da kansu ne suka buÆ™aci matafiya da direbobi su dawo su ci gaba da bin hanyar.”

Ya ce, “Daga wannan lokaci ne wasu direbobi ma su Æ™arfin hali suka fara bin hanyar, amma wasu sai dai su zagaya ta Kaduna daga Funtuwa ko Katsina idan zasu je Birnin Gwari, haka nan wanda zai zo Funtuwa ko Katsina daga Birnin Gwari sai dai ya zagaya ta Kadunan.

Duk da cewa tsohuwar Gwamnatin Buhari ta sha fitowa tana É“aÉ“atun samun nasara a yaÆ™in da take yi da ‘yan ta’adda a yankin na Æ™aramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, amma har yanzu Direbobi da matafiya na ci gaba da Æ™auracewa wannan hanya don gudun faÉ—awa hannun ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.

To sai dai ko a wannan sabuwar Gwamnatin ta Asiwaju Bola Ahmad Tinubu al’amarin zai canza a sami Æ™warin gwiwar bin hanyar? Wannan dai shi ne abin jira a gani.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment