Home Labarai INEC ta gudanar da taron Bita a Katsina

INEC ta gudanar da taron Bita a Katsina

by masta

A ranar Talata 11 ga watan Yunin wannan shekarar ne Hukumar zaɓe ta ƙasa (Independent National Electoral Commission INEC) ta gudanar da taron Bita a Katsina.

Taron bitar da ya shafi bangarorin jami’an hukumar na Dindindin da na wucin gadi, a faɗin jihar domin tattauna matsalolin da kuma irin Nasarorin da aka iya samu, saboda zaɓe na gaba.

Da yake zantawa da manema labarai, Kwamishinan hukumar zabe na jihar Katsina Farfesa Yahaya Ibrahim Makarfi, ya ce irin wannan taron bitar ana gudanar da shi a kowace jiha domin gano matsaloli da aka fuskanta alokacin gudanar da Zaben kuma a tattauna yanda za’a magancesu, a wasu zabuka masu zuwa. Inda ya bayyana cewa daga bayanai da aka samu daga ma’aikatan hukumar ne za a iya ƙara inganta zaɓukan nan gaba.

Taron da ya gudana a Muhallin ɗakin taro na hukumar Inec a garin Katsina ya samu halartar masu ruwa da tsaki a Aikin zaben 2023 na dindindin da na wucin gadi da ya gudana a watannin baya.

Source

Katsina City News

Related Posts

Leave a Comment