Home Labarai Malamin Malamai Malam Mininyawa Kano

Malamin Malamai Malam Mininyawa Kano

by masta

MALAMAI MAGADA ANNABAWA
Tare da
Bilkisu Yusuf Ali

An samo wannan rubutun ne daga Malam Babangida A Maina Founder Tijjaniyya Media News

Sheikh Malam Mijinyawa cikakken sunan sa Sheikh Abubukar Muhammad Abdullahi Tijjani.

Sheikh Mijinyawa cikakken dan jihar Kano ne, an haife shi a shekara 1313 kafin zuwan turawa kasar kano da shekara takwas (8).

Babban Malamin Yayi rubuce-rubuce da dama a bangaren addinin Musulunci kamar Fiqhu, Nahwu, Tafsir, Lunga da sauran su. ya bada gudumawa sosai don yada addinin Musulunci a yammacin Africa tare da amfanar da dukkan al’umma wurin zamantakewa, mu’amala da kuma rayuwa.

Tarihin ya tabbatar da cewa lokacin da Sharif Muhammad Alami Yazoo Najeriya a shekara ta 1923, Malam Mijinyawa shine yake masa tarjama zuwa yaren Hausa tare da sakatare.

Sheikh Abubukar Mijinyawa ya rasu a ranar 4/03/2/1946 wanda yayi dai-dai da 11/03/1366 an masa makwancin sa a jihar kano.

Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi, Allah ya kara masa kusanci da Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH.

Related Posts

Leave a Comment