Daga
Jaridar Katsina City News
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tare da hadin guiwar mafarauta da ’yan banga sun kai wani samame a kananan hukumomin Batsari da Jibia na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya raba wa manema labarai a Katsina.
A yayin farmakin, rundunar ta samu nasarar farmakar wasu sansanonin ‘yan bindiga a kauyukan Marake, Garin Yara, da Garin Labo na karamar hukumar Batsari, da kuma wani sansani na Audu Lankai, wani fitaccen dan bindiga ne da ya addabar karamar hukumar Jibia.
A cewar sanarwar, rundunar ta OC Anti-kidnapping Unit da OC SIB ne suka jagoranci aikin.
Ya ce, an kawar da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne guda biyar a yayin samamen. Haka kuma an kama wani Abubakar Idris, wanda ake zargin dan fashi ne.
Hakazalika, an kwato shanu talatin da takwas, tumaki arba’in, da awaki sittin da biyar.
Rundunar ta yi kira ga al’ummar jihar da su rika taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai a yunkurin da ake na kawo karshen miyagun laifuka a jihar.

