Home Labarai Shugaban Kasa Alh Bola Ahmad Tinubu ya Tsige Emiefele daga Gwamnan babban Bankin Nijeriya take!

Shugaban Kasa Alh Bola Ahmad Tinubu ya Tsige Emiefele daga Gwamnan babban Bankin Nijeriya take!

by masta

Daga

Aliyu Samba

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar, Mista Godwin Emefiele, CFR daga aiki ba tare da bata lokaci ba.

Hakan ma kunshe cikin wata sanarwa da Willie Bassey, Daraktan Bayanai ya fitar a madadin Sakataren Gwamnatin Tarayya a yau.

Umarnin dai ya biyo bayan bincike da ake yi a ofishinsa ne da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi da tattalin arzikin kasar.

An umurci Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin sa, wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar har sai an kammala bincike da gyara.

Related Posts

Leave a Comment