
Gwamnan Jihar Katsina Ya Ziyarci Cibiyar Nazarin Harkar Tsaro ta Kasa dake Abuja, domin Kawo Karshen Ta’addanci A Jihar Katsina.
Gwamna Malam. Dikko Radda PhD ya Kai ziyarar ne domin jaddada aniyarsa na tabbatar da Samar da tsaro, rayukka da kare dukiyoyin al’ummar jihar Katsina, Wanda hakan na daga cikin alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabensa.
Lokacin da Gwamnan yake bayyanama, kwamandan Cibiyar Nazarin Tsaron ta kasa, Mista A.S Adeleke Fni, mni makasudun kawo mashi ziyarar yace” Bani da wani guri a cikin Gwamnatina illa inga al’ummar Jihar Katsina sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya Kara da cewa” Gwamnatinsa a shirye take domin Bada dukkan wani goyan baya da suke nema abasu, domin Mutanenmu na karkara su koma noma da kiyo a cikin bbirtalolinsu da gona kansu, a kuma kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar.
Dr. Dikko Radda ya kuma Kara bayyana masu cewa” a kokarin da gwamnatin jihar ke yi, ta shirya sake fasalin tsarin tsaron Jihar, ta hanyar daukar matasa aiki tare da Horas dasu domin kara inganta tsaro, saboda haka yake rokon cibiyar da ta shigo taba Gwamnatinsa gudummuwar da ta dace don cimma Nasara.
Da yake nashi jawabin Kwamandan cibiyar ya yi wa Gwamnan karin bayani game da shirye-shirye daban-daban da Cibiyar ke bayarwa, kamar shirin wayar da kan al’umma kan tsaro, Binciken Sirri, da kuma Gudanar da yaki da ta’addanci.
Bayan haka gwamnan ya halarci bikin yaye dalibai karo na 3 na hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) da kuma tsaron jiragen sama. Wadanda suka halarci taron sun hada da Kwamandan Cibiyar da Manajan Darakta FAAN, Kabir Yusuf Muhammed da dai sauransu.
An gabatar da zaman tare da bikin yaye daliban a hedikwatar Cibiyar da ke babban birnin Tarayya Abuja, Ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, 2023,
Isah Miqdad
SSA Digital Media
09th June, 2023.

