Home Labarai Hattara da yan Damfara

Hattara da yan Damfara

by masta

Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta samu nasarar kama wasu matasa da ake zargin sun kware wajen damfarar jama’a ta hanyar tura mu su Alat na bogi bayan sun yi siyayya a wajensu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan shiya ta daya SP Abubakar Zayyanu Ambursa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jihar Kano.

SP Ambursa ya ce , sun karbi korafi daga wajen wani mutum, tun a shekarar 2022 da cewa wadanda ake zargin sun yi masa Alat na bogi kimanin kudi naira miliyan hudu da dubu dari bakwai bayan sun sayi kayan gini a wajen sa. mutum ya ce ‘’bayan sun yi mun Alat din sai daga baya naga an kwashe kudin .

Binciken yan sandan ya kai ga kama wani mai suna Alkasim Muhammad mai lakabin Bauni da kuma Dahiru Muhammad da ake kira da Gwaska.

Wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa sun kware wajen cutar al’umma ta hanyar tura musu Alat na bogi , inda daya daga cikin su ya ce yana aikata laifin a kwaryar birnin Kano.

Haka zalika yan sandan sun sake cafke wasu matasa biyu da suke da alaka dana farko da suka hada da Mubarak mai lakabin Maigaskiya da kuma Bashir Zainu.

A karshe kakakin rundunar yan sandan shiya ta daya ya ce da zarar sun kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci

Muhsin Tasiu Yau
Idon Gari

Asabar
3/6/2023

Related Posts

Leave a Comment