ƊANGOTE YAZO LEGAS BA SHI DA KOMAI
– Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, fitaccen attajirin ɗan kasuwa Alh. Aliko Ɗangote ya zo jihar Legas ba shi da ƙomai, amma ya gina daula a cikin shekaru arba’in da biyar 45.
Bayanin hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci ƙaddamar da katafariyar matatar mai ta Aliko Ɗangote a birnin Legas (Ikko).
Haka nan Aliko Ɗangote ya ce, ƙwarin gwiwa haɗi da goyon bayan da ya riƙa samu daga shugaba Muhammadu Buhari ne yasa shi buɗe matatar man, ba don haka ba da tuni yayi watsi da ita. A cewarsa.
An kashe maƙudan kuɗaɗe har dala biliyan ashirin ($billion 20) wajen gina wannan matatar mai, kimanin Naira Trillion 9 da biliyan 216.
Daga: Nafiu Salisu


