Home Labarai Rayuwata na cikin hatsari

Rayuwata na cikin hatsari

by masta

RAYUWATA NA CIKIN HAƊARI

Tsohon Fira-Ministan ƙasar Pakistan Imran Khan ya bayyana cewa, rayuwarsa tana cikin haɗari.

Imran Khan wanda tsohon Fira-minista ne a Pakistan, kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin musulmin ƙasar, ya sha fitowa a kafafen watsa labarai da jaridu yana sukar ƙasashen Yahudawa masu cin zarafin musulmi.

Malam Imran Khan ya ƙara da cewa, matuƙar yana raye ba zai daina ƙalubalantar duk wani wanda zai ci zarafin musulmi ba.

Ko a baya-bayan nan ma, Fira-ministan ya fito ya soki wasu ƙasashen da suke cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W), in da ya ce ba za su zuba ido ana cin zarafin Annabi S.A.W su yi shiru ba.

Imran Khan na ɗaya daga cikin Fira-Ministan ƙasar Pakistan da suke cire tsoro suyi magana, su ƙalubalanci duk wanda ya taɓa musulmi a ƙasar.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment