Home Labarai WANI RAGO YAYI ƁATAN DABO A CIKIN WATA RUFAFFIYAR MOTA.

WANI RAGO YAYI ƁATAN DABO A CIKIN WATA RUFAFFIYAR MOTA.

by masta

Wani Rago Da Aka Saka A Bayan Wata Mota Yayi Ɓatan Dabo

Ɓatan kaya a cikin mota ba sabon abu ba ne, musamman ga waɗanda suka saba yin tafiye-tafiye a cikin motocin haya. Inda a kan samu ɓatan kayan fasinja. A wasu lokutan wani kan manta ya ɗauki kayan wani ya bar nasa idan an sauke shi a hanya, musamman idan kayan yayi kala ɗaya, a yayin da wasu kuma suna sane suke aikata hakan. Wannan dalilin ne yasa za ka ga fasinja na saukowa suna zuwa duba kayansu a bayan mota a lokacin da aka tsaya sauke wasu fasinjojin a hanya.

To sai dai a wannan karon ba kaya ne suka ɓata a cikin motar ba, Rago ne aka sako cikin but ɗin mota aka ɗaure but ɗin, amma koda aka buɗe sai aka tarar babu shi babu alamarshi.

Al’amarin ya faru ne a safiyar yau Alhamis, inda wani direban wata mota ƙirar Bus da a ke kira da (Hummer) Homa, ya ɗauko wani Rago a bayan motarsa zuwa Kano, amma koda a ka zo Kano sai aka nemi Ragon aka rasa.

Direban motar wanda ya taso daga garin Bauchi da safiyar ya, ya shaidawa wakilin IDON GARI cewa, tunda aka rufe Ragon a bayan mota (cikin but) ba a buɗe but ɗin ba, kuma babu wanda ya ce musu but ɗin ya buɗe ballantana a ce ko faɗowa yayi a lokacin da ake tafiya.

Haka kuma, direban motar ya ce tunda suka taso ba su tsaya a wani gidan mai ko waje an buɗe bayan motar ba, kuma ya ce ko a can Bauchin ba su taso ba sai da Ragon a bayan mota, amma abinda ya basu mamaki, koda suka shigo tashar filin parking a nan Kano, ana buɗe bayan mota sai suka ga babu wannan Rago.

Shima mutumin da yake da Ragon, ya ce abin yayi matuƙar ɗaure masa kai, ta yadda yana tsaye aka rufe bayan motar da Ragon a ciki, sannan ya shiga cikin motar ya zauna. Amma abinda ya ba shi mamaki shi ne, da suka zo Kano cikin tasha aka duba babu Ragon, ya ce abin ya zame masa tamkar a cikin shirin fim.

Related Posts

Leave a Comment