‘Ƴar Takarar Gwamna A Adamawa Aisha Binani Ta Janye Ƙarar Da Ta Shigar Kan INEC
Alfijr ta rawaito ƴar takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Adamawa, Aisha Dahiru Ahmed, wacce aka fi sani da “Binani,” ta janye karar da ta shigar a kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC a yau Laraba.
Ƴar takarar ta APC ta roki kotu da ta sake duba hukuncin da INEC ta yanke na soke sanar da ita da a ka yi tun da fari a matsayin wacce ta lashe zaɓen da Kwamishinan Zabe na jihar, REC, Hudu Yunusa Ari ya yi.
Lauyan Binani, Mohammed Sheriff, a ci gaba da sauraren karar, ya shaida wa mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa ya shigar da buƙatar daina ci gaba da shari’ar, sabo da haka kotu ta yi watsi da ƙarar.
Mai shari’a Ekwo ya tunatar da Sheriff cewa an bayar da umarni a ranar da aka dage zaman da ya gabata inda aka umurce shi da ya yi magana a kotu kan ko kotu na da hurumin sauraren karar ko ba ta da shi.
Lauyan wanda ya shaida wa kotun cewa batutuwa da dama sun taso tsakanin ranar da aka dage shari’ar zuwa yau, ya roki a ba su umarnin soke karar.
Sai dai alkalin kotun ya ce tunda Sheriff ya gaza bin umarnin kotu, abin da ya dace ya yi shi ne ya yi watsi da ƙarar.
“Na ba da umarnin yin watsi da wannan kara,” in ji Justice Ekwo.

