Home Labarai Sanata Barau Ya Rabawa Malaman Makarantu Kayan Taki ,  Ciki Har da Malaman Tsangaya

Sanata Barau Ya Rabawa Malaman Makarantu Kayan Taki ,  Ciki Har da Malaman Tsangaya

by masta

A ranar 15 ga Satumba, 2025, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Senata Barau I. Jibrin, ya raba buhunan taki 4,691 ga malaman makarantu na firamare, sakandare da kuma malaman makarantar Tsangaya a ƙananan hukumomi 13 na yankin Kano ta Arewa.

Wannan rabon an gudanar da shi ne a unguwar masana’antu ta Sharada, kuma yana cikin wani shiri na ci gaba da taimakawa gwamnatin tarayya wajen samun isasshen abinci a ƙasa.

A jawabin da ya aike ta hannun Shugaban Ma’aikatansa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah, Senata Barau ya ce manufar wannan shiri shi ne a ƙarfafa wa malamai guiwa, kasancewar suna da rawar gani sosai a ci gaban al’umma.

Ya ce:

“A baya mun raba sama da buhuna 40,000 na taki ga manoma a fadin jihar Kano. Yanzu kuma muna ba wa malaman addini (Alarammomi), malaman Tsangaya, shugabannin makarantun sakandare da firamare.”

Ya ƙara da cewa an raba takin kyauta ne ba tare da sai an biya wani abu ba, kuma ya roƙi masu amfana da su yi amfani da kayan cikin hikima da amana, bisa tsarin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tabbatar da tsaro a fannin abinci.

Ga yadda aka raba kayan:

Malaman makarantar Tsangaya (Alarammomi): buhuna 661

Malaman sakandaren ƙasa (junior secondary): buhuna 221

Malaman babbar sakandare (senior secondary): buhuna 392

Malaman firamare: buhuna 227

Sauran buhunan za a raba su ga wasu rukuni-rukuni na al’umma

Shugaban ƙungiyar shugabannin makarantu a yankin, Musa Auwalu Gwarzo, ya nuna godiya tare da yabawa Senata Barau, yana cewa:

“Hakika, wannan wani babban jagora ne na kowa da kowa.”

Related Posts

Leave a Comment