Home Labarai Babban Mataimaki Na Musamman Ga Shugaban Ƙasa Kan Yaɗa Labarai, Malam Abdulaziz ya gina banɗakuna (toilets) a makarantar Fagge Special Primary School.

Babban Mataimaki Na Musamman Ga Shugaban Ƙasa Kan Yaɗa Labarai, Malam Abdulaziz ya gina banɗakuna (toilets) a makarantar Fagge Special Primary School.

by masta

Yin ginin ya biyo bayan kiran da shugaban makarantar ya yi zuwa ga Malam Abdulaziz Abdulaziz kan buƙatar wannan aiki a lokacin taron tsoffin ɗalibai na makarantar, in da nan take ya amsa kira tare da yin alƙawarin zai yi aikin.

Cikin yardar Allah an kammala aikin cikin nasara, in da aka yi aiki mai cike da inganci.

Ba wannan ne karon farko da Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ke gudanar da ayyukan alheri ga al’umma ba, domin kuwa ko a watannin baya ya kawo Intervention a makarantar sakandare ta Day Science, hakanan ya ɗauki horas da matasa sama da mutum 50 ilimin fasaha tare da bai wa ɗalibai masu hazaƙa kyautar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer Laptop) duk a ƙoƙarin sa na ganin matasa sun samu ilimi.

Bai tsaya anan ba ya ɗauki ɓangaren samar wa da al’umma ayyuka domin dogaro da kan su, ko a watannin baya ya samar wa da wasu mutum huɗu masu ƙananan ƙarfi aiki a hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS).

Allah ya saka masa da alheri.

Ibrahim Imam Abubakar
Satumba 10, 2025.

Related Posts

Leave a Comment