
Mataimakin shugaba Nijeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar na nan daram – kai da fata a kan haramcin gwajin makaman nukiliya.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da tawagar hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ƙarƙashin jagorancin sakataren zartarwarta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Nijeriya kamar sauran ƙasashen Afirka da dama na fama da tarin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziƙi da suka haɗa da fatara da talauci da sauyin yanayi.
Ya ce yanzu babban abin da ke gaban Afirka shi ne ta ga ta shawo kan matsalolin da ke barazana ga wanzuwarta – na fatara da kuma tasirin sauyin yanayi, amma ba batun mallakar makaman nukiliya ba.
A nashi ɓangaren jagoran tawagar hukumar, Dr Robert Floyd, ya yaba da ƙoƙarin Nijeriya wajen cimma muradun hukumarsa.
Sannan kuma ya yaba da shugabancin Najeriya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen bayar da gudummawar rage gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya, kamar yadda ya ce.
Post navigation
Previous:Ana shirin naɗa tsohon gwamnan Oyo, Ladoja a matsayin Olubadan na Ibadan
Next:

