371
Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Musulman Najeriya murnar zagayowar bikin Mauludin Annabi Muhammad SAW.
Shugaban ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen koyi da kyawawan halaye da karantarwar Manzon Allah.
“Yayin da muke bikin Mauludi, ya kamata mu yi duba kan irin rayuwar da Annabi Muhammad ya yi, wadda ke cike da tsarki, tausayi, kyautatawa da kuma jin ƙai, dole ne mu yi kokarin ganin mun yi koyi da wadannan kyawawan halaye.” Inji shi.
Shugaba Tinubu ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su sadaukar da ranar Mauludi domin yi wa kasa addu’a da kuma tausayawa juna.


