Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matuƙar damuwarsa game da ambaliyar ruwan da shafi wasu sassan Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekarun baya-bayan nan ta raba dubban mazauna yankin tare da yin barna kamar ofishin gidan waya da asibitin koyarwa na Maiduguri.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar, musamman ga iyalan da suka rasa dukiyoyin su, sakamakon iftala’in da ambaliyar ruwan ta haddasa.
A bangare guda kuma, hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da tantance irin barnar da ambaliyar ta yi, shugaban ya yi kira da a gaggauta kwashe mutanen daga yankunan da abin ya shafa.
Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Babagana Umara Zulum cewa Gwamnatin Tarayya a shirye ta ke ta ba da haɗin kai don wajen samar da kayayykin buƙatun jin ƙai ga mutanen da abin ya shafa.
Ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa da ta gaggauta agazawa wadanda ambaliyar ta shafa.


