Wani Ibtila’i da ya afku a ranar Lahadi yayin da mutane 48 suka mutu sakamakon fashewar wata tankar man fetur da ta afku a hanyar Bida-Agaie-Lapai- a jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya.
Abdullah- Baba-Arah, Darakta-janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Neja (NEMA) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar ranar Lahadi.
Ya ce hukumar ta samu rahoton wata mummunar fashewar tankar mai da ta afku a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na safe a kan babbar hanyar Bida-Agaie-Lapai.
A cewarsa, wurin da Ibtila’in ya afku na da nisan kilomita biyu daga ƙauyen Dendo da ke karamar hukumar Agaie a jihar Premium Times Hausa ce ta rawaito
Ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar mai dauke da mai (PMS) ta yi karo da wata tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil jihar Kano a kan hanyar Legas.
Baba-Arah ya ce wasu motoci guda biyu, wata babbar mota da wata motar daukar kaya suma abin ya ritsa da su cikin lamarin.
Ya bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane sama da 30, tare da babbakewar shanu sama da 50 suka rasa rayukansu


