Home Labarai SHUGABA TINUBU YA UMARCI MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA A KAWO ƘARSHEN ƘARANCIN MAN FETUR A NAJERIYA

SHUGABA TINUBU YA UMARCI MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA A KAWO ƘARSHEN ƘARANCIN MAN FETUR A NAJERIYA

by masta

A yayin da yake cigaba da gudanar da ziyarar aiki a ƙasar China, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya umarci mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima a gaggauta kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man fetur a ƙasar.

A rahotan da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, mataimakin shugaban ƙasar, ya gudanar da zaman tattaunawa a madadin shugaban ƙasar tare da babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗo, ƙaramin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri.

Gami da shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, Malam Mele Kolo Kyari, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz, da kuma shugaban hukumar adanawa da rarraba albarkatun mai na ƙasa, NMDPRA, Ogbugo Kalu Ukoha.

Zaman ya gudana yau a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Related Posts

Leave a Comment