Home Labarai Mafi Ƙarancin Albashi: Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kuɗi na N99b

Mafi Ƙarancin Albashi: Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kuɗi na N99b

by masta

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kwarya kwaryar kasafin kudi na Naira Biliyan 99 domin baiwa gwamnatin jihar damar aiwatar da mafi karancin albashi da wasu ayyukan.

Shugaban majalisar dokokin, Alhaji Jibril Falgore, ya ce kasafin zai baiwa gwamnatin jihar damar biyan mafi karancin albashin da kuma gudanar da ayyukan raya kasa.

Sannan ya godewa ‘yan majalisar saboda amincewa da kasafin ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa a ranar 20 ga watan Agusta ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar kwarya kwaryar kasafin na Naira Biliyan 99.

Tun bayan sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi na Naira dubu 70, jihohi da dama suka fara kafa kwamitin aiwatar da kasafin.

Jihar Adamawa ce dai, ta zamo ta farko wajen fara biyan mafi karancin albashin.
Source
Daily Nigerian

Related Posts

Leave a Comment