Home Labarai Gwamnan jihar Sakkwato Alh Dr Ahmad Aliyu ya karbi bakuncin Ministan tsaro na kasa da Kuma Shugaban rundunar tsaro ta Nijeriya.

Gwamnan jihar Sakkwato Alh Dr Ahmad Aliyu ya karbi bakuncin Ministan tsaro na kasa da Kuma Shugaban rundunar tsaro ta Nijeriya.

by masta

Gwamnan na Sokoto ya ce "Na karbi bakuncin Mai Girma Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da kuma Shugaban Rundunar Tsaro ta Najeriya, Janar Musa Christopher, wadanda aka umurta su koma Sokoto a kokarinmu na magance matsalar tsaro a yankinmu.

Da muka karbi mulki, mun gano cewa magance kalubalen tsaro a jihar mu shine babban abu da ya kamata mu mayar da hankali akai, domin duk mun san cewa ba za a iya samun ci gaba a cikin yanayi mai cike da rashin tsaro ba.

Mun kasance, kuma za mu ci gaba da gudanar da taruka kowane mako tare da hukumomin tsaro na jihar don samun sabbin bayanai kan halin da jihar mu take ciki.

Matsalar tsaro ba ta dace a bayyana komai bainar jama’a ba; lamari ne da ke bukatar sirri.

Ina kira ga al’ummar jihar Sokoto da su daina siyasantar da matsalar tsaro, domin wadannan ‘yan fashi ba sa bambanta tsakanin mambobin jam’iyya a cikin ayyukansu na zalunci.

Ina son in mika godiya ta ta musamman ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa wannan aikin da aka ba Ministan, da kuma hukumomin tsaro da suka koma Sokoto don kawar da ‘yan ta’ada a yankinmu"

Related Posts

Leave a Comment