478
Yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na samar da cikakken garambawul a fannin amfani da ma’adinan a kasar ya samu gagarumin ci gaba, inda gwamnatin Ostireliya ta amsa tayin za ta bayar da horo ga kwararrun Najeriya a fannin ma’adanai da albarkatun ƙarƙashin ƙasa,
Babbar jami’ar Australiya a Najeriya, Leilani Bin-Juda ce ta sanar da hakan a wata ziyara da ta kai wa ministan bunkasa ma’adanai Dr. Oladele Alake a Abuja.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa, haɗin gwiwar zai mayar da hankali ne kan haɓaka ƙwarewa da ilimin ƙwararrun Nijeriya don fahimtar ma’adanai da dabaru da hanyoyin da za a bunƙasa fannin domin ciyar da ƙasar gaba
Daga jaridar a yau .


