Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin yin amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi wajen tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun samu wadatattun kayan aiki domin tunkarar kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta.
Shugaban ya furta hakan ne ta bakin Mataimakinsa Kashim Shettima wanda ya wakilce shi a wajen bikin yaye manyan hafsoshin soji ‘yan ajin 32 da suka sami karin horo kwalejin tsaron kasa a Abuja.
Sanata Kashim Shettima ya kara da cewa shugaban ya amince da mahimmancin samar da kyakkyawan jagoranci a matsayin ginshikin makamin magance matsalolin tsaro da samar da ci gaban Najeriya.
Shugaban ya kuma yaba wa daliban da aka yaye bisa gudunmawar da suke bayarwa, musamman a bangaren bincike da bayanan da suka samar kan yadda za a yi amfani da harkar haƙo ma’adinai wajen samar da tsaro da ci gaban kasa Najeriya.






