Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ministan Labarai da Haɗin kan Ƙasa, Mohammed Idris ya yi kira ga ƙungiyoyin gidajen jaridu na ƙasa-da-ƙasa su ke yin adalci wajen ruwaito labaran da su ka shafi Nijeriya a kowane matakin na harkar jarida.
Idris ya yi kiran ne a lokacin da Mataimakin shugaban gidan BBC, Johnathan Munro da tawagarsa suka ziyarce shi ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce, tsarin gudanarwa ta gwamnatin Shugaba Tinubu a ɓangaren harkar yaɗa labarai ta na nan wajen bai wa al’umma yancinsu na watsa labarai tare samar da cigaba a gare su.
Ya ƙara da cewa, gidajen jaridu na ƙasa-da-ƙasa su ke ruwaito labarai cikin kula musamman ga ababen da suka shafi Nijeriya, ya na mai nuni da yin adalci a cikin hakan.
Ya kuma yaba wa ƙoƙarin wakilan gidan jaridar kan yadda suke ruwaito ayyukan cigaba da gwamnatin Tinubu ke yi da nasarori da ake samu.
Kazalika, ya jinjina wa BBC a ƙoƙarinsa na inganta ayyukan ƴan jarida da ke aiki da gidajen jaridun gwamnati tare da yin kira ga kwaikwayon irin haka daga gidajen jaridun ƴan kasuwa.


