Home Labarai Gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce ta al’umma mai son cigaban ‘yan Nijeriya

Gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce ta al’umma mai son cigaban ‘yan Nijeriya

by masta

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar shirin kafa cibiyoyin kera kayayyakin gine-gine da ake amfani da su wajen gine-gine a shiyyoyi shida na Najeriya.

Za a kafa cibiyar shiyyar Kudu maso yamma a jihar Ogun, kudu maso gabas a jihar Abia, kudu maso kudu a Warri ko Asaba dake jihar Delta, Arewa ta Tsakiya a Ajaokuta dake jihar Kogi, Arewa Maso Yamma a Jihar Kano, sai kuma Arewa maso gabas a jihar Gombe.

Wannan cibiyoyi zasu samar da ayyukan yi ga dubban matasa a faɗin ƙasar, a lokaci guda kuma zasu rage tsadar kayayyakin gine-gine da ake shigo da su Najeriya. Haka zalika za a samu damar kera kayayyakin gine-gine a nan cikin gida Najeriya da kuma kara haɓaka tattalin arziƙin Kasar.

Ababen da a samar a cibiyoyin sun haɗa da Kwanon Rufi, Silin, tiles da ƙofofi.

Related Posts

Leave a Comment