Sokoto a Yau
Tare da
Bilkisu Yusuf Ali
A yau gwamnan jihar Sakkwato ya kaddamar da motoci mallakar jihar wadanda za su ke zagayawa tsakanin jihohi don jigila da Kuma wadanda za su ke daukar iyaye mata su kadai a jihar. Wannan ba Karamin hange ne da Kuma mutunta iyaye mata da tausayawa gwamnan ya Yi ba. Sannan ya Nuna cewa mata suna da muhimmanci ba wai a iya zabe ba hatta bayan an Yi zabe an Kai gaci to tabbas da su za a Sha romon dimukaradiyya.
Yayin kaddamar da motocin Mai girma gwamnan ya Yi jawabi me ratsa zuciya inda yake cewa " Ina son in yi amfani da wannan dama in shedama al’ummar Jihar Sokoto cewar, Motocin Iyaye Mata za su cigaba da daukar Iyayenmu mata domin saukakamasu akan fanni na zirga zirga.
Hakika muna Alfahari na ganin cewar Iyayenmu Mata sun samu kulawa ta musamman karkashin gwamnatinmu kuma zamu cigaba da tabbatar da cewar wadannan motoci na Alfarma sun kula da bukatun Iyaye mata.
Tabbas, Iyayenmu Mata sun cancanci su hau kowace irin mota domin mutuncinsu da girmansu da kuma kimarsu garemu sun wuce tsadar ko wace irin mota komai tsadarta"
An Yi taro lafiya an kammala lafiya.






