Sarkin Arewan Katsina Hakimin Jibiya Tarihin sa da Kirarin sa.
Tuwo ka dade kana zamani, Jikan Dikko Sarkin Arewa.
Riga tana ga sarkin Arewa, Doki yana ga sarkin Arewa, Kyauta tana ga sarkin Arewa, Mulki yana ga sarkin Arewa.
Sarkin Arewan Katsina Hakimin Jibiya Alh Rabiu Ibrahim yayi sarauta daga 1957 zuwa 2010.
Sarkin Arewa Alh Rabiu Dane ga Gatari Ibrahim kuma jika ga Gatari Duma. A zamaninsa ne aka kirkiro karamar hukumar Jibiya kuma a zamaninsa ne aka gina madatsar ruwa ta Jibiya, kuma A zamaninsa ne aka gina babbar Asibiti, yana daga cikin Hakimai (11) da aka zaba sukayi hawan Dabar a lokacin da shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya kawo ziyara a Katsina a shekarar 1991 lokacin masarautar Katsina tanada Hakimai 25, shi jikane na sarkin Katsina Muhammadu Dikko bangaren mahaifiya kuma yayi Auren Zumunci da diyar sarkin katsina Sir Usman Nagogo.
An Ciro daga
Katsina City News
muna addua Allah yajikan magabatanmu


