Home Labarai Gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya bude masallacin Juma’a a CAS

Gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya bude masallacin Juma’a a CAS

by masta

A yunƙurin Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na bunƙasa manyan makarantun gaba da sakandire, ranar juma’a, mun buɗe Masallacin Juma’a a Kano State College of Education and Preliminary Studies (CAS, Kano) tare da Islamic Centre, wacce zata maida hankali wajen cigaban al’ūmma ta hanyar addini musulunci.

Centre zata maida hankali wajen fannin tattalin arziki, zamantakewa, da kuma cigaban ɗan Adam. Haka zalika, masallacin zai maida hankali wajen warware matsalolin da suke damun al’ūmma na yau da kullum. Amma ko kaɗan bazai shiga matsalar aƙida ta rikicin addini ba. Saboda hakanema muka zaɓo limamen daga kowane ɓangaren aƙidu domin ya zama tsari na musamman.

Ga jerin sunayen su kamar haka:

1. Dr. Sale Kumurya (Dean School of Languages).
2. Mal. Ahmad Tijjani Hassan (Ph.D. Islamic studies in view).
3. Mal. Balarabe Shehu Kabara.(Laboratory Technician).

Irin wannan yunƙurin, zai kawowa musulmai haɗin kai, da kuma nuna cewa masalahar cigaban al’ūmma da muhalli shine mafi a’ala. Irin huɗubobin da za’ayi sun kunshi dabarun tattalin arziki da kawar da talauci, tunani mai kyau, inganta karatun mata da karesu, taimaka musu wajen yin aiki da kasuwanci, gudummawar ƴan vigilant wajen haɓaka tsaro, tsafta a zamanance, hakin iyaye, yan’uwa, abokanan arziki, taimakon al’umma da ƙarfafa gwiwa da sauransu.

Kuma a wannan rana mun kaddamar da kwamitin manya wanda suka ƙunshi tsofaffin shugabannin makarantar, domin cigaban CAS. Muna godiya ga tsohon Gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu bisa gudumar da ya bayar. Allah Ya karbi ibadunmu

Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata
Komishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano
11 Maris, 2024/ 1 Ramadan, 1445

Related Posts

Leave a Comment