Home Labarai TSAKURE DAGA LABARAN DA SUKA FI BIRGE NI A YAU

TSAKURE DAGA LABARAN DA SUKA FI BIRGE NI A YAU

by masta

1 “Dokokin kundin tsarin Mulkin kasa na gaba da Muryoyin korafin tsirarun jamaa” A cewar Jagoran Kuliya manta sabon Najeriya wato Cif Jastis.

2 Mataimakin Shugaban kasa Alh. Kashim Shattima kuwa ya bi sahun Malaman makaranta wajen daukar alwashin ganin an inganta walwalarsu a wa’adin Mulkin Tajdidin Kyakkyawan Fata da suke jagoranta.

3 Atiku Abubakar kuwa ya yi kira ne ga Injiniya Kwankwaso da Peter Obi da su hakura da fatansu na zama shugabannin Najeriya su mara wa Mafarkinsa na shekaru ashirin Baya mai taken Atiku Is kwamin wanda ya ki kememe ya tabbata kuma me mafarkin ya ki ya farka.

4 Shi kuwa Shugaban kasa Asiwaju Ahmadu ya kara dukufa da aiki wajen ganin ‘yan Najeriya sun gani a kasa nan da watanni shida. Don haka ya ce a baku hakuri, duk fushin da kuke yana sane, kuma kuna da gaskiya, abubuwa babu dadi, amma a daure a kara masa lokaci

5 A gefe guda an Hango Tsohon Shugaban kasa Janar Buhari na barza dariya bayan da ya kammala kallon hirar Alhaji Atiku da ‘yan jaridu, a zatonsa Alhaji Atikun zai yi wa ‘yan kasa jawabi ne kan yadda Asiwaju ya samo shaidar karatunsa, amma sai ya ji Atikun ya bige da bayani kan yadda ya nemi a bar wa Tinubu Jahar Lagos a shekarar 2003, Don Tinubu ya ba shi goyon bayaa 2007 amma sai Tinubun ya mara wa Marigayi kuma Shugaban Kirki wato Alh. Umar Yar Aduwa baya maimakon Atikun” Shugaba Buhari ya ce: Gaskiya ka ba da ni. Ashe ma abin duk ba don Najeriya ake ba, biyan bashi ne? Ka ji wata Sharholiya!”

6 Ita kuwa Kasar China cewa ta yi Allambaran ba da ita ba! Maimakon bata wa ‘yan kasarta lokaci akan shaidar karatun wani kamar yadda wasu marasa kishin Najeriya ke yi, gara su dukufa wajen kirkirar gidan-Tafi da gidanka wanda anjima zan dora shi a manhajar Reel idan akwai me saye.

Ku yi hakuri! Fassara ce kawai tawa, sai kuma dan hoton da na sanya hana rantsuwa! Daga
Sayyada Rahma Abdulmajid

Related Posts

1 comment

Abba Adamu July 28, 2025 - 6:18 am

Ina son labarunku soboda kwarewarku Nagode.

Reply

Leave a Comment