Wakilin Mai Alfarma sarkin Musulmi prof. Junaidu Sambo wali (wazirin sokoto), ya jagoranci Taron Bude Babban masallacin juma’a na Gaya.
Taron ya samu Halartar manyan sarakuna masu daraja ta Daya Guda (9) Dake Arewa cin kasar Nan, da Kuma wadanda suka turo wakilci,da Kuma wasu daga cikin manyan attajiran kasar nan.
Da yake jawabi Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf Wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi prof. Ibrahim Jibrin, ya yabawa Mai martaba sarkin Gaya bisa irin kokari da kishin addini Daya nuna wajen Ganin kammaluwar aikin Gyaran masallacin.
A nasa jawabin Mai martaba sarkin Gaya Alh(Dr) Aliyu Ibrahim CNA, NIM, CPA (kirmau Mai Gabas),yace ” wannan Gyaran masallacin ya biyo bayan duba da yadda yakai kusan shekara arba’in (40) da Gina shi, shiyasa muka Gyara shi domin ya zamo dai-dai da zamani”
Sarkin ya Kuma yi Godiya ga mutanen da suka Bada gudun muwar su wajen Ganin an kammala aikin masallacin tare addu’ar komawar bakin da suka Halarci Taron Gida lafiya.
Allah ya taimaki sarki , ya karawa sarki lafiya. Amen.
Comr. Ubaliyo Falalu Gaya
S.A Media Gaya Emirate
29/9/2023.






