Home Labarai ‘Yan sa kai sun hallaka ‘yan ta’adda 7 a Daren jiya

‘Yan sa kai sun hallaka ‘yan ta’adda 7 a Daren jiya

by masta


‘YAN SA KAI SUN HALLAKA ‘YAN TA’ADDA 7 A DAREN JIYA.

Daga Yahaya Mahi

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 12:00 na daren jiya Lahadi Inda gungun ‘yan ta’addar suke kokarin shigowa ta wani kauyen Gidan Rabo dake gundumar Modomawa ta karamar hukumar Birnin Magaji jahar Zamfara adai dai lokacin da ake tsaka da sharara ruwan Sama.

Shigowar su kauyen keda wuya suka fara harbe harbe, inda nan take su kuma ‘Yan sa kan kauyen suka fice daga kauyen domin yi masu kwantan bauna.

Bayan sun kammala aika aikar suka harbi Mutane 2 da kwashe dinbin dukiya, sun kama hanyar ficewa kauyen kenan sai ‘yan sa kan suka bude masu wuta. Nan take suka Hallaka 7 daga cikinsu.

Shi dai wadannan hare haren ‘yan fashin Daji ya jima yana lakumar dinbin rayuka al’umma inda kullum Gwamnatoci ke cewa tana nan tana iya bakin kokarinta domin lalubo hanyoyin Dakile Samarin.

Har ye Zuwa rubuta wannan labarin babu wata hukuma data ce uffan ko taje domin jin bahasi akan faruwar Lamarin.

Related Posts

Leave a Comment