Home Labarai Tsadar Rayuwa na kara taazzara

Tsadar Rayuwa na kara taazzara

by masta

TSADAR RAYUWA

Yadda Tsadar Rayuwa Ta Jefa Al’umma Cikin Ƙunci

Halin da al’umma ta samu kanta na tsadar rayuwa, mummunan al’amari ne da aka jima ba a gani ba a Nijeriya, tun bayan mulkin Buhari na lokacin Soja a shekarar 1982.

Koda yake a wannan karon ma za a iya cewa sanadin mulkin nasa ne a Gwamnatin farar hula da ya hau a shekarar 2015 ya shafe tsawon shekaru takwas na da alaƙa da halin da ake ciki yanzu, kamar yadda da dama wasu ‘yan ƙasa suke bayyanawa.

In da wasu ke alaƙanta tsadar rayuwar da ake ciki yanzu da mulkin Buharin, wanda suka ce babu kyakkyawan salon shugabanci a cikinsa.

A yanzu haka dai wasu mutanen kan wuni su kwana da yunwa a sakamakon rashin abinci da kuma rashin kuɗin saye. Yayin da wasu ke alaƙanta hakan da canjin kuɗin da tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi, da kuma tsadar man fetur da a yanzu ya kai Naira 650 lita ɗaya a farashin Gwamnati, yayin da ‘yan bumburutu suke siyar da lita a kan Naira 800.

Wannan mawuyacin hali da a ke ciki yasa da dama daga cikin magidanta fitowa suna yin bara a titina tare da yara, musamman iyaye mata. Yayin da ‘yan kasuwa suke danganta ƙarin kuɗin kayan masarufi da tsadar mai da kuɗin mota.

A yanzu haka dai ba kowanne gida ba ne a ke iya ɗora tukunya sau uku ba a rana, yayin da sau biyun ma yayi wahala. Wanda hakan yasa talakawa suke ji a jikinsu.

Sai dai ɓangaren masana na danganta hakan da karyewar tattalin arzikin ƙasa da faɗuwar darajar Naira, kamar yadda Dr. Umar Usman na jami’ar (Madibbo Adama University, Yola) ya bayyana.

Ya ce, “Karyewar tattalin arziki da faɗuwar darajar Naira, da juyin mulki da ƙasar Nijar rayi, duk suna ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo ƙaruwar yunwa a Africa ba iya Nijeriya kaɗai ba…”

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment