
Gwamna Abba K Yusuf na Jihar Kano yakai ziyarar ta’aziyya Garin Gunduwawa Karamar Hukumar Gezawa bisa rasuwar Marigayi ALHAJI MUHAMMAD INUWA SHITU daya daga cikin Alhazan Jihar Kano da Allah yaywa rasuwa a kasa Mai tsarki (MAKKAH) bayan kammala hajjin bana na shekarar 2023.
Gwamna Abba K. Yusuf ya Sami Wakilcin Darakta Janar na Hukumar Alhazan Jihar Kano ALH. LAMINU RABI’U. A Jawabinsa LAMINU RABI’U yayi ta’aziyya ga iyalan Marigayin tare da Adduar Allah ya jikansa yasa Yana Aljanna Amin.
A karshe D.G. Laminu Rabi’u ya Mika sakon Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Abba K. Yusuf da Mataimakinsa Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo na KUDI DA KAYAN ABINCI ga Iyalan Mamacin.
Har ila yau, Alh. LAMINU RABI’U ya sake wakiltar Gwamnan Kano EXCELLENCY Abba K. Yusuf a Karamar Hukumar Gaya domin ganawa da Iyalan ALHAJI UMAR MUSTAPHA Wanda yanzu haka ke kwance a asibitin Makka na Sarki Abdulaziz sakamakon rashin lafiya Wanda mukewa Adduar Allah ya bashi lafiya ya dawo wajen iyalansa Albarkar Shugaban halitta (S A.W.).
A karshe D.G. Laminu Rabi’u ya Mika sakon Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Abba K. Yusuf da Mataimakinsa Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo na KUDI DA KAYAN ABINCI ga Iyalan majiyyacin.
mujitaba na biu

