
Gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta samar da filaye da biyan diyyar kudi ga mutane 421 da aikin fadada filin jirgin saman Umaru Musa Yar’adua ya shafi kadarorinsu.
Gwamnatin jihar Katsina ta hannanta wurin da za a kara fadada filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke jihar ga ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban Sakatare a ma’aikatar kasa da safiyo ta jihar Nasiru Ibrahim Yar’adua, ta ce filin ya kai fadin murabba’in kadada wato ‘hekta’ 76.40Ha don kara fadada wannan filin jirgi ya zamo tsara a idon duniya.
Kwamishinan kasa da Safiyo na jihar Katsina, Dr Faisal Umar Kaita, da ya karbi bakuncin tawagar jami’ai daga ma’aikatar sufurin jiragen sama, Abuja, ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta yi nasarar biyan diyya ga mutane 421 da za a yi amfani da filaye da gonakinsu don kara fadada filin jirgin saman.
Dr Faisal Umar Kaita ya ce Malam Dikko Umaru Radda ya raba wa mutanen filaye da kuma biyansu kudin diyyar da suka haura Naira milyan 280.
Shugaban tawagar gwamnatin tarayya daga ma’aikatar sufurin jiragen sama, Mr Clement Olayinka, Daraktan Bunkasa Jiragen Sama na Ma’aikatar sufurin sama ta tarayya, ya yi godiya ga gwamnatin jihar Katsina da ta samar da wannan wuri da za a fadada filin jirgin saman.
A ranar 4 ga watan Mayun, 2023, Sanata Hadi Sirika wanda shi ne ministan sufurin jiragen sama a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da aikin fadada filin jirgin saman da zai lakume bilyoyin Naira.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Alh. Usman Isyaku ne ya wakilci Gwamnan Jihar Katsina wajen kaddamar da bada takardun shaidar filayen ga Gwamnatin Tarayya.
SSA Isah Miqdad,
3/8/2023.

