Ba a rago daga zaune , don haka ma ake cewa in ka ji wane ba banza ba. Sanin wa ye Arc. Ahmad Musa Dangiwa shi zai Kara tabbatar wa da al’ummar Nijeriya cewar an yi hange da aka zabo shi.

Daga
Malam Abdurrahma Aliyu
1. An haifi Arc. Ahmed Musa Dangiwa a shekarar 1963 yanzu Yana da shekara 60 daidai
2. Haifaffen garin Kankiya ne, a Jihar Katsina.
3. Ya yi karatun firamare a garin Katsina da Kankiya da Bindawa da Malumfashi.
4. Ya yi makarantar sakandire a Makarantar tunawa da Sardauna (Sardauna Memorial Callege)
5. Ya halarci makarantar share fagen shiga jami’a (CAS Zaria) daga bisani ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria inda ya samu digirinsa na farko a fannin kimiyyar zane da tsara gidaje ( Bsc Architectural Science)
6. Daga baya ya sake komawa ABU din inda ya samu shaidai kammala karatun digiri na biyu (Msc )
7. Yayi bautar kasa a Jihar Cross Rivers dake kudancin Nijeriya.
8. Ya yi aikin gwamnati na dan takaitaccen wa’adi a shekarar 1988 inda yayi koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina(HUK poly), da kuma ma’aikatar lafiya ta Jihar Katsina.
9. Ya bar aikin gwamnati ya tsunduma aiki da kamfanoni masu zaman kansu
10. Shi ne Jarman Kankiya
11. Daga bisani ya kafa nasa kamfani mai suna AM Consult Wanda a karkashinsa ya gudanar da ayyuka masu dunbin yawa a fadin Nijeriya
12. Ya shigo siyasa a shekarar 2003 a karkashin jamiyyyar ANPP
13. Yayi takara a matakai daban-daban
14. Yana daya daga cikin mambobin kwamitin rukon kwaryar jamiyyyar CPC na jihar Katsina da uwar jam’iyyyar ta kasa ta turo karkashin kantoman ruko Faruk Adamu Aliyu
15 Shi ne shugaban Jam’iyyyar APC na farko na jihar Katsina
16. Ya rike mukamin Manajin Darkta na Bankin Bayar da Lamunin Gina Gidaje na kasa karkashin gwamnatin Shugaba Buhari daga 2017 -2022
17. Shi ne Darkta janar na kwamitin yakin zaben APC na shekara ta 2023 a Jihar Katsina
18. Mutum ne shi mai akida mai hakuri da kawaici
19. Mutum ne shi da ya shahara wajen rike amanar abokan siyasa, daga shekara ta 2003 zuwa 2011 an san shi tare da Engr Nura Khalil, bayan da Nura ya koma Jamiyyyar PDP, Dangiwa ya sake kulla amana da tsohon Gwamnan Jihar Katsina Rt.Hon. Aminu Bello Masari, har zuwa karshen wa’adin mulkinsa. Wadanda suka san shi sun ce bai taba kulla alkawari ya warware ba, ko a cikin dadi ko cikin wuya, sai dai kai ka warware .
20. Ba a taba bashi aiki ya kasa aiwatarwa ba, ko a Bankin Bayarda Lamunin Gina Gidaje an ga irin kwazonsa inda a cikin shekaru biyar kacal ya kafa tarihin da ba’a kafa ba a shakaru 42 na kafuwar bankin.
Shi ne sakataren gwamnatin jihar Katsina daga ranar 31 ga watan Mayu 2023 har zuwa yau 27 ga watan Yuni da aka aika sunanshi a matsayin wanda za a tantance mukamin Minista daga jihar Katsina.

