Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya gana da sabon shugaban jami’ar nazarin ayyukan kiwon lafiya ta tarayya Prof B.B Shehu.
A lokacin ganawar da ta gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin samar da wurin da jami’ar za ta zauna na wucin-gadi tare da ba da matsugunai ga ma’aikatan da za su yi aiki a jami’ar.
Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa duk inda aka kafa wannan jami’a, za a samu wani asibitin da za a bayar domin tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata.
Da yake mayar da jawabi, sabon shugaban jami’ar Prof B.B Shehu ya ce ya ji dadin yadda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya tarbe su.
Ya na da tabbacin cewa wannan jami’a za ta zama abin alfahari ga al’ummar jihar Katsina ganin cewa jami’a ce da ta jibinci kiwon lafiya kawai.
Prof B.B Shehu ya ce jami’a ce da za ta rika horar da aikin malaman jinya, likitoci da sauran bangarorin da suka danganci kiwon lafiya da hakan zai ba da dama a samu wadatuwar malaman asibiti a ba a jihar Katsina kadai ba, a Nijeriya bakidaya.
Ya ce jami’ar na daga cikin sabbin jami’o’i 6 da gwamnatin tarayya ta ba da umurnin a kafa a shiyyoyi 6 na kasar nan.
SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
25/7/2023.


