349
APC A YAU
Daga
Bilkisu Yusuf Ali

Ba abin mamaki ba ne don an ji Injiniya Abba Kabir Bichi ya dau alkawarin biyan kudin makaranta don kuwa yana jerin farko a kasar nan na Danmajalisar da yake kyautatawa al’ummarsa da Kayan more rayuwa da tallafi a kasar nan. Halin tausaya da Jin Kai na Abba Bichi ya sa ko a guguwar jam’iyyar NNPP me mulki a Kano haka ta bar wannan kujera Tsamiya tsada ko gezau. Kai hatta yan adawa da jam’iyyar APC da Abba ke ciki ba su iya butulcewa alherinsa ba. Don haka wannan alkawarin da ya yi na biyawa daliban BUK kudin makaranta ya yi abin da ya Saba yi ne taimako sannan ya yi shi a lokacin da ya dace duba da yadda kudin jami’a a wannan lokacin ya yi tashin gwauran zabi.

