
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa ‘yan jihar Kano cewa nan da makwanni biyu ne asibitin kananan yara na Hasiya Bayero zai koma bakin aiki, kamar yadda ya umarci kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran don tabbatar da maido da cibiyar lami lafiya.
Gwamnan ya fadi wannan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda ya kai masa ziyarar Sallah, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da aiwatar da manufofin haihuwa kyauta yadda ya kamata.
Wanda wannan kudiri yana cikin kudurorin gwamnatin da ta Ayyana tun a lokacin yakin neman zabe. Gwamnan ya kuma nanata kudurin jam’iyyar NNPP wajen gudanar da aiki tare da nuna damuwa kan tsaftar muhalli a jihar.
Ya kuma baiwa ‘yan majalisar ministocinsa da su hada kai da shuwagabannin kansilolin kananan hukumomi daban-daban domin gano al’amura masu mahimmanci.
Abba ya kalubalanci masu suka da su rika ajiye bayanan aikinsa, su kuma yi masa hukunci bayan ya kammala wa’adinsa, kuma ya yi mamakin dalilin da ya sa duk wani mai mulki zai iya daukar dukiyar al’umma ya mayar da ita don amfanin kansa.
Sarkin Gaya ya shaida wa gwamnan cewa masarautar ta yi kwakkwarar kwarya-kwaryar taka tsantsan don kara karfafa tsaro.
Kamar yadda Hisham Habib Kakakin Gwamnan Kano ya wallafa.

