Home Labarai Rashin Dasa bishiyoyi da kananan Tafkuna na Barazana ga Al’ummar Jihar Kano

Rashin Dasa bishiyoyi da kananan Tafkuna na Barazana ga Al’ummar Jihar Kano

by masta

GARIN KANO A YAU | RASHIN YAWAITAR BISHIYOYI DA KANANUN TAFKUNA BARAZANA CE GA AL’UMMA.

Daga: Jamilu Iliyasu Bichi.

Garin Kano na fama da yawan ababan hawa da masana’antu wadanda suke fitar da gurbatacciyar iska da ake kira a turance “Air Pollution” ita wannnan iskar tana gurbata muhalli wadda ake kira a turance “Global Warming” ko dumamar yanayi a harshen hausa.

Shiyasa mutumin da yake zaune a wajen garin Kano yafi wanda yake cikin kwaryar birnin Kano shakar lafiyayyar iska, sannan zafin da akeyi a birnin Kano yafi wanda ake a wajen garin Kano.

Babban abinda yake yakar wannan dumamar yanayin shine samar da yawan bishiyoyi da kananun tafkuna da suke samar da iska, bishiyoyi suna shakar wannan iskar da ababan hawa da masa’antu suke fitarwa wadda ake kira a turance “Carbon” mu kuma sai su bamu “Oxygen”.

Idan ka dauki cikin Birnin Kano a yau akwai karancin bishiyoyi da wadannan kananun Tafkuna kusan duk an cikesu anyi shaguna, ba’a samun wadatacciyar iska, ga yawaitar ababan hawa da masana’antu da suke fitar da gurbatacciyar iska Al’umma suna shakewa.

Tun a zamanin baya Gwammatin Kano karkashin Gwamna Abdu Bako tayi nazarin faruwar hakan shiyasa ta dukufa wajen samar da manya-manyan Dam, gidan adana namun daji da ta kewayeshi da bishiyoyi ciki da waje iskar wannan Dam din data samar da bishiyoyin gidan namun daji da daidaiku data shuka a cikin garin sun taimakawa Al’ummar Kano a wancan lokacin duk karancinsu inka hada da na wannan zamanin da Kanon ta cika.

A yanzu birnin ya cika ya bunkasa da yawan Al’umma da ya kamata ace ansamu karin bishiyoyi da kananun tafkuna a cikin garin amman kullum wadanda ake dasu ma raguwa sukeyi ana sare bishiyoyi ana yin shago ana cike tafkuna ana yin shaguna.

Shekarun baya da suka wuce tun daga Titin Tsohuwar Jami’ar Bayero inka taho har zuwa Kofar Nassarawa zaka ga irin wadannan kanunun Tafkunan Kofar Famfo,Hauren Wanki, Hauren Shanu, Kofar Na’isa, ‘Dan Agundi da Kofar Nassarawa amman yanzu kusan duk sun zama Tarihi.

~Jamilu Iliyasu Bichi
Mazanarcin kasa da Muhalli daga Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Related Posts

Leave a Comment