ADABI
TARE DA
AMINA HASSAN ABDUSSALAM ( AHA)

IDON GARI: Hajiya Zuwaira za mu so mu ji dan takaitaccen tarihin rubutunki.
Amsa : Ni ma’abociyar karance karance ce, musamman litattafan turawa, daga bisani na faɗa na hausa wanda har ta kai ga naji a raina ya kamata nima na fara rubutun ko zan cimma burina na ganin na isar da saƙo ta hanyar da nake so.
IDON GARI: A yan watannin nan an ga kina rubutun fadakarwa a facebook akan aure har kina yi wa kanki da lakabi likitar ma’aurata. Me ya ja hankalinki zuwa wannan bangaren?
Amsa : Eh na daɗe ina neman hanyar da zan dinga wayar da kai cikin sauƙi bayan ta hanyar littafi musamman kan zamantakewa wanda a yanzu abubuwa da dama kan taka muhimmiyar rawa wajan lalata aure, wanda gyaran kaɗan ne in akayi za’a samu fahimtar juna . kwatsam kuma sai ga social media wadda da yawa rabin makaranta suna bibiya wanda baya basu da kafar tattaunawa da marubutansu sai yanzu da zamani ya zo, ganin haka ya sa nayi caraf na ke amfani da wannan damar. Kuma Alhamdulillah kwalliya na biyan kuɗin sabulu. Dan ba zan iya ƙiyasta adadin ma’auratan da suka daidaita ta sanadin hakan ba. Waya da saƙon text ma ba a barni ba a taƙaice har gida ake biyoni wani lokacin ma ina dawowa daga aiki kafin na huta na faɗa kan wani case ɗin. Sai dai muce alhamdulillah Allah ya dubi niyyarmu.
IDON GARI: Wasu suna ganin cewa rubutun naki yana ba wa maza kariya ne, wai ba kya irin abin nan da ake cewa balancing a turance, me za ki ce ga wannan zargi?
Amsa :Ai ni mace ce, kuma duk wata kalma da zan ji an jefi mace da ita dole ta zafafa zuciyata in har na san ciwon mata ƴan uwana. Mace ita ce a ƙasa abu kaɗan za ta aikata wanda zai iya tarwatsa duk tarin tubalin ladan data gina. Ba ta mazan nake ba ta mata nake su san laifukansu su gyara in suka yi haka, wallahi duk bala’i da masifa na miji sai dai ya yi ya gama. Mace uwa ce dan me zan sakaya laifukanta shi ya sa na zaɓi a baje a faifai.. Kuma wasu ne basu adalci amma in ta kama na taɓa mazan ma ina taɓawa aini ban ɗauki ɓangare ba.fahimtar juna kawai nake so a samu a zaman aure.
IDON GARI: Dangane da kare maza an ce wai neman mijin kike shi ya sa kike kare mazan. Haka ne ko akwai wani dalili na daban?
Amsa :Hahaha, Eh mijin ma in na nema ai ba laifi bane. Abinda na sani kawai shi ne komai na da nashi irin tarin ƙalubalen… Tunda irin wannan fassarar aka yi min ni kuma ina roƙon addu’ar da zanyi a amsa min. “Allah ya hukunta ni da abinda ke cikin zuciyata” dan shi ya san sirrin kowacce zuciya
IDON GARI: A irin wadan nan rubuce –rubuce kwanakin baya kin yi wani rubutu da ya yamutsa hazon facebook inda ki ka ce kashi 70 na matan aure suna neman maza, hakan bai yi wa wasu dadi ba, da yawan mutane sun yi miki raddi kama daga na cin mutunci da yabo da nasiha da suka, wasu kuma sun ce kina nufin kaso 70 din da ki ka ambata mazinata ne, shin a mahangarki meye bambancin neman maza da zina?.
Amsa : Wannan ya mutsi da aka samu ko gezau ko ɗar-ɗar in miki ta wani mawaƙi.. wanda suka yabeni fahimtarsu, wanda suka zageni suka aibatani, suma ya danganta da fahimtarsu ke marubuciya ce da kika san a salo na rubutu akwai wajan da baki buƙatar ɓarin kalma wajan faɗin ra’ayi. Na yi magana a dunƙule an ce ba haka ba, na ɗakko hanyar warwarewa dalla dalla an sake jan zare… Shi ya sa na tanƙwashe hannuwana. Neman maza da zina amsar a bayyane take, gaba ɗaya sukan iya amsa suna a siga ɗaya, in aka yi wani juyin kuma kowanne da muhallinshi kamar yanda na ce Neman maza su kuma da yake zinar ce a ransu sai suka ɗauki wancan layin amma da kin bibiyi post ɗina bayan wannan zaki ga masu aikata neman maza cikakkiya 20% ƙididdiga ta basu .sannan ban kira sunan gari ba, ban kira sunan jaha ba, ba kira sunan kabila ko addini ba, Abu ne a dunƙule kaso 20 na aikata cikakkiya, wani kaso 20 ɗin suna ɗaukar salo na sharar fagen shiga, kaso 30 nasu kalar salin daban in kika haɗa jumulla 70 kenan. Amma ba wai gaba ɗayan 70 ɗin ake nufi ba.
IDON GARI: Akwai ma wadan da suka ce kin cancanci a yi miki bulala 80 saboda kazafin zina, yaya ki ka ji haka a ranki?
Amsa : Hahaha abin da naji a raina dama suna da niyyar in sun samu dama ace haka kawai an bulaleni may be ko na takura musu . To su bari na aikta laifin tukunna.
IDON GARI: Mu koma kan batun alkaluman kididdiga na mata manema maza, wane mizani ko madora ki ke da ita wajen fidda alkaluman kason da ki ka ambata domin da yawa sun koka da cewa wannan tsantsar ra’ayinki ne ba bincike ne ya nuna haka ba? Ko kuma iya matan da ke kewaye da ke ke naman maza shi ya sa kika yi jams’u?
Amsa : na baki amsar wannan ai kuma a sama. Muje wata tambayar
IDON GARI: An ce akwai wadan da suka bukaci ki janye rubutunki amma kika ki, maimakon haka sai ki ka yi wa abin kwaskwarima, duba da cewa mai rubutu yana tare da kuskure, kin yarda kin yi kuskure wajen fidda adadin kason mata 70?
Amsa : ba wai naƙi janyewa bane. Wa nake tsoro da zan janye ba tare da na baje abun a faifai ba. Ni ina kan bakana fa, kije ki bincika ko su su bincika 20% wallahil azim da aurensu suke aikata neman maza 20% za ki same su suna chart da mazaje musamman ta hanyar bayyana wasu daga surorin jikinsu, 30 % kuwa a bayyane yake ba sa zinar amma suna soyayya da wasu mazan, kallo da kalaman da bai dace ba ga wanda ba muharraminta ba, kwalliyar da zata ɗauk hankalinsu da sauransu, in kika haɗa jimullar 70% fa kenan.( Hypothesis) su faɗaɗa bincike.
IDON GARI? Yaya batun neman suna ko shahara da aka ce shine makasudin rubututtukan nan?
Amsa : meye kuma neman Suna, me sunan zai min in na nemeshi ?aikin dake gabana ma ya isheni takura da matsinshi yafi yawa a cikin neman suna. Amma abinda na sani shi ne Allah shi ne mai lokaci.
IDON GARI: A karshe maimakon gyara ba kya tunanin alkalaminki zai iya haddasa fitina tsakanin ma’aurata?
Amsa : bana fatan hakan ta kasance ina ƙoƙarin tsarkake zuciyata kuma ina roƙon Allah da ya yi riƙo da hannayena.
Malama Zuwaira Idon Gari na godiya.
A cigaba da bibiyarmu a www.idongari.Com

