Daga Wakililanmu
Tare da
Muhsin Tasi’u Ya’u
Kungiyar Tijjaniyya Grassroots mobilization and Employment of Nigeria ( TIGMEIN) reshen jihar Kano ta Mika sakon Taya murna ga zababben gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa lashe zaben gwamnan na jihar Kano da ya yi. Yayin Zantawa da shugaban Kungiyar na jiha da ya yi da wakilan jaridar Idon Gari. Coordinator din Alh Bello Liman ya nuna godiya ga Allah da kuma nuna murnarsa Kasancewar Allah shi ke ba da mulki kuma shi ya zabi Abba. Sannan kowa yasan shugaban kumgiyar na Kasa Shehu Tijjani Sani Auwalu irin jajircewar da ya yi kan tabbatuwar wannan nasara ta Abba. Sannan Uban wannan kumgiya shi ma Sarkin Kano na goma Sha hudu Kuma Khalifan Tijjaniya Khalifa Sunusi Lamido Sunusi shi ma ya yi kokari matuka don kafa wannan kumgiya da tsayuwarta da kuma Kishiinsa ga jihar Kano. Don haka wannan Taya murna ta bangare uku ce ‘ muna taya Injiniya Abba Kabir Murna sannan jagoranmu Shehu Tijjani Sani Auwalu sannan Khalifanmu na Tijjaniya Khalifa Sunusi na biyu. Allah ya Taya riko Allah ya yi riko da hannayen shugabanninmu Amin, mun gode.’


