134
Rundunar Sojin Nijeriya ta Kammala Gina Sabuwar Makaranta a Tudun Biri
Rundunar Sojin Najeriya ta kammala gina sabuwar makarantar firamare a Tudun Biri, Jihar Kaduna, a matsayin tallafi ga al’umma bayan kuskuren harin bam da ya faru a 2023. Kakakin rundunar, Lt. Col Musa Yahaya, ya ce an gina makarantar ne domin farfado da al’umma da kuma ba wa yara ingantaccen ilimi. Gwamna Uba Sani ya yaba da aikin, yana mai cewa zai inganta ilimi da zaman lafiya a yankin. Sabuwar makarantar na dauke da dakunan karatu, azuzuwan zamani da wuraren shakatawa, don karfafa iyaye da al’umma wajen tura yara makaranta da kara hadin kai tsakanin sojoji da jama’a.





