Sojoji sun fatattaki wani harin Yan Ta’addan Ƙungiyar ISWAP a Bama dake Jihar Barno
Sojojin Operation Hadin Kai sun fatattaki wani harin da mayakan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP/JAS suka kai a gaban sansanin FOB Miyanti da ke ƙaramar hukumar Bama a Jihar Barno.
Majiyar da ta tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) daga Hedikwatar Sojoji ta ce harin ya auku ne da safiyar ranar 18 ga Nuwamba.
Majiyar ta ce karin dakarun da aka turo daga 21 Special Armoured Brigade sun yi luguden wuta mai ƙarfi wanda ya tilastawa mayakan su ja da baya, lamarin da ya bai wa sojoji damar sake ɗaukar cikakken iko da sansanin.
A wani lamari dabam, sojojin Bataliya ta 192 da 26 Task Force Brigade sun amsa kiran gaggawa daga manoma a Warabe da Sava-Dure a ƙaramar hukumar Gwoza, inda yan ta’adda suka kai hari kan manoman.
A cewar majiyar, a sauran sasannin arewa maso gabas, rundunonin sojoji na ci gaba da ayyukan fatattakar ’yan ta’adda karkashin Operation Desert Sanity IV ba tare da wani fuskantar cikas ba.
A Arewa maso Yamma kuwa, sojojin 4 Demo Battalion da 11 Field Engineer Regiment da ke aiki a karkashin Operation FANSAN Yamma sun gano sabon wurin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wajen Fatika a kan hanyar Dogon Dawa–Old Kuyello a ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Daga baya sojojin sun yi artabu da wasu ’yan bindiga uku da suka tsere a Gobarawa da Nachibi, inda suka kwato babura guda biyu da aka bari.
A Jihar Filato, dakarun Operation Enduring Peace (OPEP) sun shiga lamarin kisan mutum ɗaya da aka yi a yankin Riyom, tare da ceto wani direba da ’yan fashi suka yi garkuwa da shi a kan hanyar Bokkos–Barkin Ladi.
Majiyar ta ce bincike da farautar waɗanda suka aikata laifukan na ci gaba da gudana.


