Home Labarai SHUGABAN SOJAN ƘASA YA ISA GUSAU, JIHAR ZAMFARA

SHUGABAN SOJAN ƘASA YA ISA GUSAU, JIHAR ZAMFARA

by masta

Shugaban Sojan Ƙasa, Lieutenant General Waidi Shu’aibu, ya isa Gusau domin ziyarar aiki a Jihar Zamfara.

Janar Shu’aibu ya kai ziyara ne zuwa Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Fansa Yamma da ke Zamfara, a ci gaba da rangadin aiki da yake yi a yankunan gaba-gaba.

Da isowarsa, manyan kwamandoji suka tarbe shi tare da ba shi gaisuwar ban girma ta musamman daga Rundunar Guard of Honour.

Shugaban Sojan Ƙasa na tare da wasu manyan jami’an soji, ciki har da wakilai daga Shugaban Rundunar Ruwa da Shugaban Rundunar Sojin Sama, da sauran manyan jami’an tsaro.

Related Posts

Leave a Comment