Home Labarai Gwamnan jihar Sokoto Dr Ahmad Aliyu Sokoto ya taryi tawagar mataimakin shugaban kasa da ya kawo wa Iyalan Shagari taaziyya

Gwamnan jihar Sokoto Dr Ahmad Aliyu Sokoto ya taryi tawagar mataimakin shugaban kasa da ya kawo wa Iyalan Shagari taaziyya

by masta

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Sokoto domin jajanta wa dangin Shagari kan rasuwar Hajiya Sutura Aliyu Usman Shagari.

Ziyarar ta nuna girmamawa da haɗin kan ƙasa, tare da tunawa da babban gudunmawar da dangin Shagari ke da ita a tarihin Jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan Jihar Sokoto Dr Ahmad Aliyu Sokoto ya bayyana godiya bisa wannan ziyara, yana mai cewa ta kasance muhimmin alamar tausayawa da haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma.

An yi addu’ar Allah Ya jikan marigayiya, Ya gafarta mata, ya ba iyalanta hakurin jure wannan rashi amin .

Related Posts

Leave a Comment