Mai bawa shugaban ƙasa shawara akan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za’a kawo karshen rashin tsaro a ƙasar, Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Damaturu yayin da yake jajanta wa al’ummar jihar Yobe kan harin da ƴan ta’adda suka kai a jihar.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ta’addanci, inda ya ce sadaukarwar da suka yi ya haifar da ingantuwar tsaro a ƙasar nan.
Taskira – H Online Tv ta rawaito Ribadu ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana aiki ba dare ba rana don kawo ƙarshen rashin tsaro, kuma lokaci ya yi da za a tabbatar da tsaron ƙasar baki ɗaya a kau da rashin sa kwatakwata a ko ina a ƙasar nan.
Kazalika, Ranar juma’a ne dai dakarun rundunar sojin Najeriya tayi nasara halaka ƙasurgumin ɗan tá’áddá mai gidan Bello Turji wato Halilu Sububu wanda suka addabi al’ummar jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da Kebbi a ƙoƙarin rundunar sojojin Najeriya na kawo ƙarshen garkuwa da mutane a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.


